Lalatattun Kayayyakin Abinci Ƴan Najeriya Ke Bamu Kyauta — Koken Marayu

Wani gidan Marayu a Babban Birnin Tarayya Abuja mai suna Honour Ground Home ya koka akan lamarin wasu ƴan Najeriya da suke bada gudunmawar kayayyakin abinci da wasu da suka Lalace a gidan Marayun.

Dayake jawabi a lokacin da yake karɓar kayayyakin Abinci daga Ƙungiyar Matan Ma’aikatan Masu Gobara a ranar Lahadi, Shugabar Marayun Mrs Blessing Ijenwa ta Koka kan yadda Marayu a gidan suke kamuwa da rashin lafiya bayan sun ci abinci marar kyau.

Tace gidan Marayun bai taɓa tunanin cewa mutane zasu bada kayayyakin abincin da suka riga suka lalace, domin suna ganowa ne a lokacin da suka tashi zasu yi abinci, ko kuma bayan sun kammala abincin.

“Waɗannan yaran suna kuka a duk lokacin da suka karɓi abinci lalatacce daga wasu ƴan Najeriya, abin tausayi ne,” inji ta.

Daganan sai ta yabawa Ƙungiyar ta FOWA data bayar da abinci mai nagarta da suke da lafiya ga gidan Marayun.

Ijenwa tace Gidan Matsayin suna godiya da wannan gudunmuwar, amma tana so tace Lalatattun kayayyakin abinci suna cutarwa.

Sa tayi kira ga Ƴan Najeriya dasu riƙa ziyartar gidan Marayun akai-akai domin taimakawa Marayun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram