Sylva Ya Bada Kyautar Miliyan 5 Ga Waɗanda Rushewar Masallaci Ya Kaduna

Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur Timipre Sylva ya bada kyautar Naira Miliyan 5 ga Shugaban Tijjaniyya na Nguru Jahar Yobe Sheik Muhammad Alfathi Gibrima.

Wannan tallafin ya biyo bayan rushewar Masallacin sa daya kashe rayuka 4 da jikkata wasu.

Sylva ya sanar da bada tallafin ta hanyar wata tawaga mai ƙarfi daya aikewa Shehin Malamin, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jaridar Dillaliya a Kaduna Alhaji Ibrahim Gamawa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi daga Mai Taimakawa Tawagar ta fuskar Kafafen Yaɗa Labaru Dr. Musa Muhammed, yace a lokacin da yake karɓar gudunmawar, Sheikh Gibrima ya bayyana Jindaɗinsa ga Ministan da irin tausayawar sa.

Shehin Malamin yace duk da cewa shi Kirista ne daga yankin Kudu, Sylva ta nuna cewa Ƙasa ɗaya ce muke, da kuma tausayi ga Al’umma.

Ya godema Sylva da irin tausayawar sa da fatan Alkhairi ba tare da nuna wani wariya ba.

Sheikh Gibrima yace “a madadin sauran mabiya Tijjaniyya da lamarin ya shafa a lokacin rugujewar Masallacin, ina nuna godiya ga wannan tallafin kuɗi daga Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur Timipre Sylva.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram