Tsohon Gwamnan Kaduna Yace Akwai Dalilan Da Zasu Iya Sanyawa PDP Ta Sha Kaye A 2023

Tsohon Gwamnan Jahar Kaduna Mukhtar Yero yayi kira ga masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar PDP da su haɗa kansu gabanin Babban Zaɓen Shekarar 2023, domin Jam’iyyar ta samu nasara.

Yero, wanda yayi wannan kiran a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a ranar Lahadi a Kaduna, yace Jam’iyyar na iya rasa Zaɓen idan mambobin basu haɗa kan su ba.

Yace ya zama dole ga mambobin Jam’iyyar su haɗa kan su domin samun nasarar zaɓe mai zuwa a Ƙasar.

Yace “yana da mahimmanci ga ƴan PDP dasu haɗa kan su domin ceto Najeriya.

“Dole mu goge duk wani rashin jituwa tare da ajiye Son kai a gefe, tare da yin dubi akan abinda ƴan Najeriya ke so da Jam’iyyar.

“Idan Najeriya ta zama Ƙasa mai ikon kanta, dukkanin mu zamu ji daɗi, kuma zamu yi farin ciki da yanayin.

“Idan muka cigaba da yin faɗa da juna, muka inganta son kanmu, zamu ƙare a rasawa.”

Yero yayi kira ga Matasa da suyi amfani da lokacin Zaɓen Shekarar 2023 tare da gina kansu a matsayin su na Shuwagabanni na gobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram