Akwai Mutanen Sama Da Milyan 6 Masu Ciwon Talauci A Katsina – Darma

Sanannan ɗan siyasar nan kuma shugaban cibiyar PLBC, Dr Muttaqha Rabe Darma ya ce mutanen Katsina sama da milyan shida na fama da ciwon talauci.

Dr, Darma ya faɗi haka ne a yayin da ya ke karɓar baƙunci gungun ƴungiyoyin jahar Katsina da suka ziyarci ofishinsa a ranar Talatar nan da nufin roƙonshi da ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma wata don ya samu damar yi ma al’umma ayyukan alherin da ya ke son ya yi ma su.

Kalli cikakken labarin a cikin wannan hoton bidiyon da ke ƙasa.

Muttaqha Rabe ya gode ma ƙungiyoyin da suka nuna damuwarsu sosai a kanshi saidai ya ce barin jam’iyyar PDP ba mafita ba ce a wurin a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram