Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa reshen Jahar Edo tace ta lalata Gonakin Tabar Wiwi 17 da girmansu takai Safiya 15 a Jahar.
Kwamandan Hukumar na Jahar Edo Mr Buba Wakawa, ya bayyana haka a lokacin da yake tattauanawa Da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a Benin a ranar Talata.
Wakawa ya bayyana cewar an lalata gonakin ne tsakanin watan Janairun zuwa Maris.
Ya bayyana cewar a wannan lokacin, Hukumar ta rage yaɗuwar miyagun kwayoyin da girman su yakai Kilagaram 480.074.
Ya bayyana cewar miyagun ƙwayoyin da aka rage yaɗuwar su, ta ƙunshi Exol, da Tiramol, da Diazepam, da Lexotan, da Swinol da Cocaine, da Heroin, da Meth, da sauran su.
Wakawa ya ƙara dacewa, Hukumar ta kuma kama Tabar Wiwi da yawan ta yakai Kilogaram 2,349.424 a wannan lokacin.
A cikin watanni ukun, yace kuma Hukumar ta kama mutane 90 da ake zargi da laifi da suka ƙunshi Maza 80 da Mata 14.