Najeriya Na Buƙatar Wanda Zai Tsaya Tsayin Daka, Domin Yaƙi Da Matsalar Tsaro – Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce za a shawo kan matsalar rashin tsaro a Najeriya yadda ya kamata idan aka zabi mutum mai jajircewa a matsayin shugaban kasa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP a ranar Litinin a Maiduguri.

Ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta gaza wajen magance matsalolin rashin tsaro da tattalin arziki a kasar.

Wike ya ce ‘yan kasar ba za su iya zuwa gonakinsu da wasu wuraren ba saboda tsoron kada a yi garkuwa da su ko kuma a kashe su.

“Najeriya na mutuwa kuma bai kamata mu bar Najeriya ta mutu ba. Dole ne mu ceto kasar nan.

“Na yi imanin cewa Najeriya na da bege. Don haka ina son in tsaya takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP.

“A Borno kawai muke jin rashin tsaro, amma yanzu abin ya kare, yunwa ba ta san Musulmi ko Kirista ba, rashin tsaro bai san Arewa ko Kudu ba.

“Muna bukatar wanda yake da karfin gwiwa don yaki da rashin tsaro a kasar nan kuma ina so in gaya muku cewa ina da wannan karfin gwiwa,” in ji shi.

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Zanna Gaddama ya yaba wa Wike bisa kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki kan al’amuran da suka shafi al’ummar Najeriya.

Gaddama ya bukaci mabiya jam’iyyar da su marawa gwamnan baya don samun tikitin takarar shugaban kasa na PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram