Osinbajo Bazai Taɓa Zama Shugaban Ƙasa, Ƴan Arewa Zasu Kaishi Su Baro — Primate

Shugaban Cocin Evangelical Spiritual Primate Elijah Ayodele a ranar Talata ya gargaɗi Mataimakin Shugaban Ƙasa akan ƙudirin shi na tsayawa takarar Shugaban Ƙasa.

Primate Ayodele ya yabawa Osinbajo daya ayyana ƙudirin shi na takarar, yana mai cewa bazai taɓa zama Shugaban Ƙasar Najeriya ba.

A cikin wata sanarwa da Mai Taimaka masa ta Fuskar Yaɗa Labaru ya fitar, Osho Oluwatosin, Primate Ayodele yayi gargaɗin cewa matakai na gaba na tabbatar da ƙudirin shi zai haifar da lalata Dukiya, domin wasu manya-manyan mutane zasu ja dashi kuma zasu kaishi su baro.

Yace “abun a yaba ne yadda Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ayyana sha’awar sa ta tsayawa takarar Shugaban Ƙasa domin zuciyar sa ta dai-dai tu, amma bazai taɓa zama Shugaban Ƙasa ba, kawai ayyana aniyar sa yana nufin bayyana abunda ke damun sa.

“Ya rage ruwan sa ya lalata Dukiyar sa ko kuma kada yayi, amma bazai taɓa zama Shugaban Ƙasa na gaba ba. Zasu kaishi su baro, ƴan Arewa basu sin shi, kuma wasu zasu ja dashi, bazai taɓa zama ba.

“Babu wani abu na ba dai-dai ba, ga dukkanin wanda ke Son bayyana ƙudirin sa ba, amma Osinbajo bazai samu nasara ba, ya ji kunya, ko ba haka ba, Allah baya fushi da Osinbajo, amma zai lalata dukiyar sa, sabudda bai sanya ta, inda ya dace ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram