Yanzu-yanzu: Adamu, Kyari Sun Yi Murabus Daga Majalisar Dattawa
Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu a ranar Talata ya yi murabus daga mukaminsa na sanata a majalisar dattawa.
Shi ma Sanata Abubakar Kyari mai wakiltar Borno ta Arewa ya yi murabus daga Majalisar ta Dattawa.
Adamu da Kyari, a wasu wasiku daban-daban da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta, sun ce matakin nasu ya zama wajibi ne biyo bayan fitowar su a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa da mataimakinsa na kasa a yankin (Arewa).