Yanzu Yanzu: Osinbajo Zai Gana Da Ƴan Majalisar Wakilan APC A Ranar Laraba

Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo zai gana da mambobin Jam’iyyar APC a Majalisar Wakilai ta Ƙasa a ranar Laraba.

Osinbajo ya gayyaci Ƴan Majalisun Tarayya na APC a ɗakin taro ba Banquet dake Fadar Shugaban Ƙasa zuwa buɗe baki a ranar Laraba.

Mataimakin Majalisar Wakilai Ahmed Wase ya karanta takardar Mataimakin Shugaban Ƙasa a buɗe zaman Majalisar a ranar Talata.

Takardar gayyatar tana zuwa ne ƙasa da awanni 48, bayan yayi taro da Gwamnonin APC zuwa buɗe baki a daren ranar Lahadi, domin neman goyon bayan su akan ƙudirin sa na tsayawa takarar Shugaban Ƙasa.

Mataimakin Shugaban Ƙasar dai a sanyin safiyar ranar Litinin ya ayyana ƙudirin sa na tsayawa takarar Shugaban a Babban Zaɓe na Shekarar 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram