Jam’iyyar adawa ta PDP a Katsina, ta yi watsi da sakamakon zaɓe da hukumar zaɓe ta jahar Katsina ta sanar a matsayin sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin jahar.
Wannan ya fito ne daga bakin Salisu Yusuf Majigiri a lokacin da ya ke tsokaci jim kaɗan bayan kammala bayani ga manema labarai da jam’iyyar ta shirya ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin ciyaman na jam’iyyar, Salisu Lawal Uli.
Majigiri ya ce yana magana ne a madadin yan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ta PDP da suka haɗa da Sanata Yakubu Lado ƊanMarke da Aminu Yar’adua da shi kanshi Majigirin da sauransu.
Yana mai cewa kwatakwata ba a bi yadda tsarin sanar da zaɓe ya ke ba.
Don haka a cewarshi bba su yarda ba kuma zasu bi duk hanyoyin da doka ta tanada domin mashe kujerunsu da gwamnatin APC ta yi masu fashi da makami da rana tsaka a cikin watan azumi.