Mutane biyar sun ƙone ba tare da gano su ba, a yayinda Ababen hawa guda biyu yayi gaba da gaba a Nawfia, akan Babbar Hanyar Awka-Enugu ta Jahar Anambra. Motocin sun ƙone da mutanen dake ciki.
Lamarin ya faru a sanyin safiyar ranar Laraba tsakanin mota Toyota ƙirar Highlander da Lamba BMR570BE da Toyota ƙirar Hiace ba tare da Lambar Mota ba.
A cewar wanda ya shaida lamarin, Direban Motar Hiace, wanda tsaka da gudu, tayi gaba da gaba da Motar ta Highlander, inda daganan suka kama da wuta.
Mutane biyar da suka haɗa da Manyan mutane biyu, da Mata uku, sune lamarin ya rutsa dasu.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, Jami’an Kula da Gobarar, sun samu nasarar kashe Gobarar.
Jami’an dake ceton na Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa daga Shiyya ta RS5.3, Awka suna wurin domin kula da tafiyar ababen hawa, tare da cire motocin da gawar akan hanyar.
Kwamandan Shiyya na Jaha Adeoye Irelewuyi ya yi jaje ga iyalan da suka rasu.
Ya Gargaɗi masu Motoci a Jahar, dasu daina mugun gudu, tare da tsayawa a gudun da aka ƙayyade.