Shehu Sani Ya Buƙaci Dattawan Arewa Dasu Bar Buhari Ya Kammala Wa’adin Mulkin Sa

Tsohon Ɗan Majalisar Dattijai na Ƙasa Shehu Sani yaƙi amince wa da matsayar Dattawan Arewa cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka daga Mulkin sa, sakamakon yadda kula da Matsalar Tsaro na Najeriya.

Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar Ƙungiyar Dattawan Arewa a ranar Talata ta buƙaci Buhari ya sauka daga muƙamin sa, sakamakon kasa tsare Ƙasar.

Ƙungiyar ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Dr Hakeem Baba-Ahmed ya fitar, inda tace abin damuwa yadda kusan shekaru 7 a cikin ofis, amma har yanzu Buhari bashi da amsa akan matsalolin tsaro a faɗin Ƙasar.

“Gwamnatin Buhari bata nuna cewa zata iya magance matsalolin tsaro dake damun Ƙasar ba.

“Bazamu cigaba da rayuwa, da mutuwa ba a ƙarƙashin masu kisa, masu garkuwa da mutane, masu fyaɗe, da kisan ƴan ta’adda wanda suka hanamu zaman lafiya da tsaro

Dayake maida jawabi ga Ƙungiyar Dattawan Arewa a ranar Laraba, Sani wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a Majalisa ta 8, ya buƙaci Ƙungiyar Dattawan data bar Buhari ya kammala wa’adin mulkin sa.

A rubutun daya fitar a shafin sa na Twita, Shehu Sani yace idan ya kammala wa’adin mulkin sa, Shugaban Ƙasa zai samu damar shirya zaɓen Shekarar 2023.

Ya rubuta “Ƙungiyar Dattawan mu na Arewa masu mutunci nason Buhari ya sauka daga muƙamin sa, Ban yarda ba, Kubar Sai Baba ya Kammala Wa’adin Mulkin sa, ya shirya zaɓe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram