Wata Mata Ta Roƙi Dangiwa Da Ya Aurar Da Jawarawan Katsina Idan Ya Zama Gwamna

A Yau 13 ga watan 4 na shekerar 2022 Ɗan takarar Gwamna a jahar Katsina, Arc, Ahmad Musa Dangiwa, ya kai ziyara a zauren majalisar dokoki ta jahar domin sanar da su ƙudurinsa na fitowa takarar gwamnan Katsina da kuma neman goyon bayansu.

Arc, Dangiwa wanda ya ke dan jam’iyyar APC ne, ya ɗau dogon lokaci yana bayanin irin yadda ya hidimta ma jam’iyyar da jahar ta Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

Dangiwa ya bayyana yadda ya samarda gidaje ga ma’aikata da kuma kuɗaɗen don ginawa da gyara gidaje ga dimbin mutanen Najeriya musamman ma al’ummar jahar Katsina.

Da ya zo ga ƙudurorin da ya ke da su dangane da irin shirin da ya yi ma alummar Katsina, kawo hanyoyin haɓɓaka tattalin arziƙi da kiwon lafiya da ilimi da sauran abubuwa walwala da more rayuwa.

Dangiwa ya kuma yi wani alƙawari nan ta ke inda ya amsa ma wata mata roƙonta gare shi na ya sanya tsarin aurar da jawarawan Katsina idan Allah ya ba shi gwamna, inda ya ce ya ji wannan koke nata kuma zai yi hakan in Allah ya so.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram