Nan Bada Jimawa Ba, Zamu Sanar Da Waɗanda Suka Kai Harin Jirgin Ƙasa na Abuja-Kaduna – Ministan Tsaro Bashir Magashi

Gwamnatin Tarayya a jiya tace nan bada jimawa ba, zata sanar da waɗanda suka ɗauki nauyin kai harin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna.

Gwamnatin ta kuma bayyana mummunan lamarin aka abinda ya bayyana haɗin gwiwa tsakanin Boko Haram da Ƴan Bindiga dake gudanar da harin su a yankin.

Yace duk da Jami’an tsaro na yin bakin ƙoƙari domin gano Dabar data kai harin, rahoto ta nuna cewa, Ƙungiyar Ƴan bindigar tana haɗa hannu da wasu, yana mai kira ga ƴan Najeriya dasu haɗa hannu da Gwamnati domin gano su.

Idan dai za’a tuna Gwamna Nasiru El-Rufa’i na Jahar Kaduna ya bayyana cewar kai harin a Jirgin Ƙasa Ƙungiyar Boko Haram ta ɗauki nauyin kaishi, da suke aiki a tare da wasu ƴan bindiga a Kaduna, Zamfara, da Sokoto, da Niger, da Kebbi.

Da suke maida jawabi bayan taron Majalisar Zartaswa, Ministan Tsaron Manjo-Janar Bashir Magashi dana Yaɗa Labaru Alhaji Lai Mohammed sun bada tabbacin cewa tana kan gano lamarin.

Magashi a lokacin da yake maida jawabi akan ko Gwamnati ta gano waɗanda suke bayan kai harin, yace “dagaske, ina tunanin Hafsoshin Tsaro na bakin Ƙoƙarin su domin gano waɗanda suke bayan kai hari, kuma zamu gaya maku waɗanda suka kai harin nan bada jimawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram