Gwamnatin Tarayya ta ɓude ƙofar tattaunawa da ƴan ta’addan da suka sace Matafiya a Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna a watan Maris na Shekarar 2022.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta Daily Post ta bada rahoton cewa ƴan bindiga sun farmaki jirgin, tare da kashe mutane 8 da sace wasu da dama a cikin Jirgin.
Ƴan bindigar sun yi ikirarin kashe waɗanda lamarin ya shafa, idan Gwamnatin Tarayya taƙi sasantawa dasu.
Amma kwanaki tara bayan kai harin, ƴan Ta’addan sun sako Manaja-Darakta na Bankin Manoma Alwan Hassan, bayan anyi zargin sun karɓi Naira Miliyan 100.
Dasuke jawabi da Ƴan Jarida a Kaduna a ranar Juma’a, ƴan uwa da abokanan waɗanda aka sace a Jirgin Ƙasan, sun tabbatar da cewa Gwamnatin ta basu tabbacin cewa ta buɗe ƙofar tattaunawa da ƴan ta’addan.
“Bayan taron Majalisar Zartaswa na Ƙasa a ranar Laraba, mun ji Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ministan Yaɗa Labaru Lai Mohammed cewa Gwamnati ta fara tattaunawa dasu, cewa tuni ta fara tattaunawa da waɗanda suka sace ƴan uwan mu,” inji Dr Jimoh Fatai, wanda aka naɗa a matsayin Shugaban Ƙungiyar dake da rajin Sanyawa Gwamnati tayi ƙoƙari a sako ƴan uwan su.
“Muna jindaɗi akan haka, mun yaba, mun ji daɗin wannan ƙoƙarin, abunda muke roƙo shine Gwamnati ta ƙara azama a wannan ɓangaren,” Inji shi.