Manyan Aji Na Taimaka wa Ƴan Bindiga A Zamfara – Cewar Matawalle

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce kwararan hujjoji sun nuna cewa manyan masu fada a ji daga jihar na daga cikin wadanda ke taimaka wa ayyukan ’yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar.

“Wasu daga cikin wadannan mutane jiga-jigai ne da jama’a ke mutuntawa, akwai kuma daga cikin jama’ar da ke karbar ’yan kudade kadan domin bai wa ’yan bindiga bayanai,” inji Gwamna Matawalle.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamna Matawalle shawara kan harkakokin yada labarai Malam Zailani Bappa ya fitar, yace hakan ne ya sa gwamna Bello Matawalle yakan yi rantsuwa da kur’ani mai tsarki, ya kuma bukaci wadanda ke cikin gwamnatina da su yi hakan, domin nisantar da kansu daga ayyukan ’yan bindiga a jihar.

Gwamna ya kuma yi kira ga duk ’yan jihar da shugabannin siyasa da su bi sahunmu domin tsabtace kansu daga duk wani zargi na mu’amala da ’yan ta’adda.

Matawalle ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun dakile ayyukan ’yan bindiga a jihar duk da goyan bayan da suke samu daga wasu bata gari, hasalima sun yi kokarin rage kaifin hare-haren ’yan ta’dda a jihar.

“Ba sa son ’ya’yanmu su je makaranta, ba sa son mu yi tafiye-tafiye mu samu abin dogaro da kai, ba sa son mu samu zaman lafiya a gidajenmu da garuruwa da kauyukanmu, suna son mutane su yi tawaye ga gwamnatin jiha da ta tarayya. Amma ba za su yi nasara ba. Nasarar ta mu ce da yardar Allah Madaukakin Sarki”.

Gwamnan ya kuma kara jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta wannan mummunar dabi’a tare da rokon iyalan wadanda ’yan ta’addan suka sace ’yan uwansu da su amince da matakan da suke dauka don tabbatar da ceto ƴan uwansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram