Ƴan Bindiga Sun Kashe Ɗan Sanda Da Mutane 4 A Niger

Wasu daruruwan ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Gwada da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’in dan sanda guda da wasu mutane hudu.

‘Yan bindigar sun yi garkuwa da mutane da dama da kuma wasu shanu da ba a tabbatar da adadinsu ba, kamar yadda Jaridar DAILY POST ta rawaito.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a yankin mai tazarar kilomita 20 daga Minna, babban birnin jihar a yammacin ranar Asabar.

Sauran mutanen da suka rasa rayukansu a harin sun hada da mata biyu da yara biyu, dukkansu ‘yan sansanin ‘yan gudun hijira ne, wadanda ke da mafaka a sansanin ‘yan gudun hijira na Gwada da aka kora daga yankin Zumba na karamar hukumar.

Wata majiya a garin Gwada ta bayyana cewa wadanda harin ya rutsa da su sun rasa rayukansu ne a lokacin da ‘yan bindigan suka harbi motar da suke ciki a kokarinsu na tsayar da ita.

Sai dai majiyar ta ce dan sandan ya mutu ne a yayin musayar wuta tsakanin jami’an tsaro na hadin gwiwa da ‘yan bindigar.

A cewar majiyar, yayin kazamin fadan da bangarorin biyu suka yi, an kashe dan sanda daya, da kuma daya daga cikin ‘yan bindigar. Da yawa daga cikin ‘yan bindigar sun gudu da raunukan harbin bindiga, an kuma kwato babura shida na ‘yan bindigar”.

Jaridar Dimokuradiyya ta kuma tattaro cewa rundunar hadin gwiwar jami’an tsaron ta kara kaimi inda suke bin ‘yan bindigar da suka tsere.

Kokarin samun tabbatar da faruwar lamarin ta bakin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Tsaro na Jihar, Mista Emmanuel Bagna Umar ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta bakin jami’in hulda da jama’a na jihar, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kauyen Kaduna kusa da Gwada, karamar hukumar Shiroro a jiya.

A cewar Abiodun, “Rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, tare da ‘yan banga sun tattaru zuwa yankin kuma an fatattaki ‘yan bindigar”.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu ana kan zayyana bayanai game da lamarin, yayin da aka aike da karin taimako zuwa Gwada kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.

Har ila yau, babban jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, wanda ba zai so a ambaci sunansa ba, ya tabbatar da harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram