Kashi 90 na Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci A Imo, Kiristoci Ne – Uzodimma

Gwamnan Jahar Imo Hope Uzodimma yayi kira ga Mazauna Jahar dasu zauna cikin zaman lafiya domin amfanin Jahar.

Daya ke kokawa akan matsalolin tsaro a Jahar, Uzodimma yayi kira ga masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Jahar, dasu zauna cikin zaman lafiya.

Wasu Ƴan bindiga a ranar Alhamis sun kashe Jami’in Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta a lokacin shirin cigaba da bayar da Katin Ɗan Ƙasa a Isinweke ta Ƙaramar Hukumar Ihitte/Uboma ta Jahar.

A cikin wata sanarwa a ranar Asabar domin bikin Easter, Gwamnan yace ta la’akari da Azumi , Addu’o’i, bayar da kyautuka, Kiristoci su nuna irin gudunmawar su ta hanyar haɓɓaka zaman lafiya a Jahar Imo.

Uzodimma yace “abin gaskiyane, abun damuwa, cewa Kashi 90 na Masu aikata laifin, da masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Jahar Imo a dukkanin yankin Igbo, suna amsa sunan cewa su Kiristoci ne. Dagaske waɗannan Kiristocin suna bin tafarkin Christ? Suna tunawa da hukunce-hukunce na biyar.

“A lokutta da dama naje na duƙursa ga masu ɗaukar nauyin ta’addanci na Kashe-kashen nan da su ajiye Makaman su, tare da zaunawa cikin zaman lafiya da tattaunawa a dukkanin wata matsala dake gare su. Na kuma yi roƙon yafiya ga kowa da suke ganin an yiwa ba dai-dai ba, sakamakon tsare-tsare na Gwamnatin Jahar Imo wadda nake Jagoranta. Ina Son in ƙara neman wannan yafiyar, da zaman lafiya a Jahar mu,” inji Sanarwar.

Sanarwar ta naƙalto Gwamnan na cewa ya fifita jindaɗin Al’ummar Jahar Imo akan komai, a wajen Shugabancin sa a matsayin sa na Gwamna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram