Ban da Wata Jiƙaƙƙiya Da Hukumar EFCC – Ɗan Takarar Gwamnan Neja a PDP

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Neja a karkashin jam’iyyar PDP, Isah Liman Kantigi ya bayyana cewa ba shi da wata alaka da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC kamar yadda ake hasashe a wasu bangarori.

Dan takarar wanda ya yi wannan ikirari a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP, na shiyyar ta biyu dake jihar wato zone B a sakatariyar jam’iyyar da ke Minna, ya ce hukumar ta kunshi mutane ne ba ruhanai ba kuma idan aka gayyace shi, tabbas zai mutunta gayyatar da suka yi masa.

Kantigi, wanda tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar ne a zamanin tsohuwar gwamnatin Gwamna Muazu Babangida Aliyu, ya ce wannan jita-jita na cikin hasashe ne na wasu bata gari.

Inda Kuma ya Kara da cewa, “A shirye nake in kalubalanci masu yada irin wadannan jita-jita na cewa ina da wata matsala da hukumar EFCC. Kuma, EFCC ba ruhanai ba ce, ta mutane ce kuma idan an gayyace ni zan mutunta gayyatar”.

Dan takarar gwamnan ya yi kira ga wakilan da su yi watsi da duk wasu jita-jita da ba su ji dadi ba game da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram