Duk Wanda Yake Da Burin Yin Takara Yayi Yi Murabus Daga Mukaminsa Nan Take – Oyetola

Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa a jihar da ke da sha’awar tsayawa takara a zaben 2023 da su yi murabus daga nadin mukaman su ba tare da bata lokaci ba.

Wata wasika mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Oluwole Oyebamiji, ta ce wannan umarni ya ta’allaka ne kan sashe na 84(12) da 29(1) na dokokin zabe na 2022 da kuma jadawalin zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar. .

A cewar umarnin, “ Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa a jihar da zasu tsaya takara a zaben 2023 da su yi murabus daga mukamin nasu ba tare da bata lokaci ba.

“Wannan ya biyo bayan taron Majalisar Zartaswa da aka yi a ranar Laraba 13 ga watan Afrilu, 2022 da hadin gwiwar sashe na 84 (12) da na 29 (1) na dokokin zabe na 2022 da kuma jadawalin zabe da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta fitar.

“Ana ba da sanarwar ga dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar Osun da su bi umarnin Gwamna da kuma samar da doka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram