Sanata Babba Kaita Na Nuna Alamun Ficewa Daga Jam’iyyar APC Zuwa PDP

Sanata mai wakiltar shiyyar Daura a jahar Katsina da ke Arewa maso yammacin Najeriya ya yunkurin ficewa daga jam’iyya mai mulki ta APC.

Wannan labari na zuwa ne bayan da sanatan ya gana da manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP a jahar.

Babba Kaita dai ya kasance sanatan da ya fito daga shiyyar da shugaba Buhari ya fito kuma ya zama yana nuna adawarshi karara idan har aka yi wani abu da ya ke ganin mai kamata ba.

Hakazalika ana rade-radin yana son tsayawa takarar gwamnan jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram