Ƴan Fashin Daji Sun Harbe Malamin Makarantar Sakandare A Zamfara

Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton ƴan fashin daji ne sun harbe wani babban Malamin Sakandare a Jihar Zamfara

An harbe Malamin ne mai suna Tukur Kurma a lokacin da ƴan bindiga su ka bude wuta a kan matafiya a hanyar Tashar Taya, Danzaure a titin Anka-Dakitakwas-Gummi, a yammacin jiya Talata.

TVC ta rawaito cewa ƴan bindigar sun harbe motar da ke tafiya lokacin da direban ya ki tsayawa tare da wasu motocin.

Marigayi Tukur Kurma ya kasance Shugaban Fannin Tarihi a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Gummi da ke Jihar Zamfara.

Wannan lamari dai na zuwa ne kwanaki uku bayan wasu ƴan bindiga dauke da makamai sun kashe wasu mutane hudu a garin Masamar Mudi da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram