Saudiya Ta Baiwa Najeriya Kason Kujerar Hajji 43,000

Saudi Arebiya ta baiwa Nijeriya kason kujeru dubu 43 domin zuwa aikin Hajjin 2022.

Babban Sakataren Hukumar Jin daɗin Alhazai na Kano, Muhammad Abba Dambatta ne ya sanar da hakan yayin taron manema Labarai a yau Laraba.

Dambatta ya ce hakan ya biyo bayan yadda kasar Saudiyya ta ce adadin mutune Milyan daya ne kadai za su gudanar da aikin Hajjin na bana a fadin duniya.

Ya ce wannan adadi da aka baiwa Najeria na da alaka da yawan mutanen da Najeria ta ke da shi.

Dambatta ya tuna cewa ko a 2019 ma kujerun Hajji dubu 95 a ka baiwa Nijeriya amma Alhazai dubu 47 ne kawai suka je.

Babban Sakataren ya ce, ko da ya ke har yanzu Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa, NAHCON ba ta fitar da adadin kudin aikin hajjin bana ba, alamu na nuna cewa kudin zai ƙaru fiye da yadda aka biya a shekarun baya

Ya ce a baya an canja Dalar Amurka akan naira 350, in day ce yanzu kuma ta kai N408, in da hakan ke nuna lallai za a samu ƙarin kudin.

Daily Nigerian ta rawato cewa yanzu dai ana jiran hukumar NAHCON ta baiwa kowacce jiha adadin kujerunta tare da bayyana adadin kudin aikin hajjin na bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram