Tsohan Dan Takarar Majalisar Dokokin Jihar Katsina na Karamar Hukumar Sabuwa A Zaɓen Da Ya Gabata, Honarabul Ɗahiru Sufiyanu Damari,Ya Yi Kira Ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari Ya Yi Gaggawar Fitowa Takarar Dan Majalisar Dattawa Na Yankin Funtua Domin Cigaba Da Ayyukan Alheran Da Ya Saba Yi Wa Wannan Shiyyarmu Dama Jihar Katsina Baki Daya.
Honarabul Ɗahiru Sufiyanu Damari Kuma Daya Daga Cikin Mawaƙan Jam’iyyar APC Na Jihar Katsina Ya Bayyana Haka Ne A Cikin Wata Takardar Manema Labarai Da Ya Raba A Katsina Ciki Har Da Jaridar Blueink News Hausa.
Tsohan Dan Takarar Ya Kara Da Cewa Bayan Dogan Nazari Da Na Yi Tare Da Tuntubar Kungiyoyin Matasa Da Dattawa Da Ɗalibai Na Wannan Shiyyar Na Ga Ya Dace Mu Hanzarta Yin Wannan Kira Ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari Da Ya Fito Takarar Dan Majalisar Dattawa.
Kamar Yadda Ya Bayyana, Hakan Zai Baiwa Matawallen Hausar Dama Domin Cigaba Da Shimfida Ayyukan Alheri Da Bunƙasa Noma Da Kiwo Da Kuma Koƙarinsa Na Dakile Wannan Matsalar Tsaro Da Muke Fama Da Ita.
Idan Kuma Har Bai Fito Ba Akwai Yiwuwar Mu Maka Shi Kotu Har Sai Ya Amsa Wannan Kira Na Mu Saboda Cigabanmu Da Jihar Katsina Baki Daya Saboda Gogewarsa’ Cewar Asas.
Honarabul Ɗahiru Sufiyanu Damari Ya Cigaba Da Cewa Tun Da Aka Yi Jihar Katsina Ba’a Taɓa Samun Gwamna Mai Tausayi Da Daratta Dan Adam Kamar Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari Ba. Shi Yasa Sakamakon Dinbin Hujjoji Da Nike Da Su Da Kuma Tuntubar Kungiyoyin Da Na Yi, Idan Bai Fito Ba Kotu Zan Garzaya.