Kanwan Katsina Ya Taya Kabomo Murna Akan Samun Mukamin Babban Sakatare

Kanwan Katsina Hakimin Ketare Alhaji Usman Bello Kankara, ya taya Alhaji Sani Bala Kabomo murna akan samun matsayin Babban Sakatare da ya yi a Ma’aikatar Yada Labarai, Al’adu Da Al’amurran Cikin Gida ta Jihar Katsina.

Kanwan na Katsina ya taya sabon Babban Sakataren murna ne a sa’ilinda ya ziyarci Ma’aikatar tare da tawwagar shi.

Alhaji Usman Bello Kankara wanda shine Uban Kungiyar Yan Jarida Ta Kasa Reshen Gidan Talabijin na Jihar Katsina, ya bayyana nadin Kabomo a matsayin abinda ya dace, lura da kwarewar shi a sha’anin aikin kafafen yada Labarai.

Kanwan na Katsina ya tabbatar da cewar, Alhaji Sani Bala Kabomo ya yi aiki tukuru akan daga darajar gidan Rediyon Jihar Katsina, a lokacinda ya shugabanci wurin.

Daga nan sai ya yabawa Gwamna Aminu Bello Masari, akan wannan nadi na Kabomo wanda ya bayyana a matsayin wanda ya chanchanta.

Ya kuma yi addu’ar samun nasarar sabon Babban sakataren a wurin gudanar da nauyinda aka dora mashi.

Da yake maida jawabi, sabon Babban Sakataren Ma’aikatar Alhaji Sani Bala Kabomo, ya bayyana farin cikin shi akan wannan ziyara ta taya murna da Uban Kasar ya kawo Mashi.

Alhaji Sani Bala Kabomo ya bayyana Kanwan Katsina a matsayin aminin Yan Jarida wanda kuma yake bayar da dumbin gudummuwa ga aikin na Jarida a Jihar Katsina da ma Kasa baki daya.

Ya tabbatar da cewar zai yi bakin kokarin shi wurin yin aiki tukuru ta fuskar daga darajar kafafen yada Labarai mallakin Gwamnatin Jihar.

Shima a nashi jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Alhaji Abdulkareem Yahaya Sirika, ya bayyana kanwan na Katsina a matsayin mai kaunar aikin Jarida Na sahun gaba da Yan Jarida a Jihar Katsina ke alfahari da shi.

Daga nan sai ya bada tabbacin yin aiki kafada da kafada da sabon Babban Sakataren Alhaji Sani Bala Kabomo domin a cimma nasarar da ake bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram