Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta yi hasashen cewa mai yiwuwa farashin kudin maniyyatan Najeriya zai karu da sama da kashi 50 cikin 100 idan aka kwatanta da abin da aka biya a shekarar 2019.
Idan za’a iya tunawa cewa an biya kudin aikin hajjin shekarar 2019 ne a kan Naira Milliyan daya da dubu Dari biyar. don haka ana sa ran maniyyatan da suka ajiye kudi tun shekarar 2020 za su biya Karin akalla N1m.
Da yake jawabi a wajen taron da shugabannin hukumar alhazai ta jiha domin shirye-shiryen aikin hajjin 2022, shugaban hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Hassan, ya ce hasashen karuwar ya samo asali ne sakamakon yanayin tattalin arziki kasa da kuma wasu dalilai.
Ya ce, “Hasashen yana kan karuwa ne saboda a shekarar 2019, canjin kudin najeriya akan dala ya Kai Naira 306 amma yanzu zai kai Naira 410. Dukkanmu mun san cewa aikin hajji shine kashi 97 cikin 100 na kudin waje na kamfanonin jiragen sama na abinci da sauran su.
“Haka zalika, Saudiyya ta kara kudin harajin daga kashi 5 zuwa kashi 15 cikin 100. Abin da su ma suka ce sun zuba jari mai yawa a Mina da Arafa.”
Hassan ya ce, za a bukaci alhazan da su ke shirin yi musu cikakkiyar allurar rigakafin kamuwa da cutar corona, inda ya ce gwajin cutar na PCR ma ya zama dole ga kowani maninyaci
Kazalika ya bayyana cewa, cikin kujeru 43,008 da aka bai wa Najeriya, 33,976 za’a raba su ne ga jihohin, yayin da za a ware 9,032 ga masu yawon bude ido da masu zaman kansu.