Mai Mala Buni Yayi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Gaidam

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi Allah-wadai da harin da ‘yan ta’adda suka kai wa al’ummar Geidam tare da yin kira da a kara yin addu’o’in samun dauwamammen zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

Buni, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ta hannun mai magana da yawunsa, Mamman Mohammed, ya bayyana harin a matsayin mummuna, musamman a wannan wata na Ramadan mai alfarma lokacin da mabiya addinin Musulunci ke neman rahamar Allah daga aikata munanan ayyuka.

Gwamnan ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa jajircewar da suka nuna, inda ya bada tabbacin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro domin dakile miyagun laifuka a jihar.

Buni ya kuma bukaci al’ummar jihar da su rika kai bayanai masu amfani a kan lokaci ga jami’an tsaro domin inganta matakan da suka dace.

Haka nan kuma mu yi amfani da damar da watan Ramadan ya bayar wajen yi wa jiharmu da kasa addu’a,” sanarwar ta kara da cewa.

Da yake jajantawa wadanda harin ya rutsa da su, Gwamna Buni ya bada tabbacin aniyar gwamnatinsa na tabbatar da dorewar zaman lafiya, tsaro da cigaba a fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram