Gwamnan Jahar Rivers Nyesom Wike ya shaidawa Wakilan Jam’iyyar PDP a Jahar Taraba, cewa idan Jam’iyyar ta bashi Tikiti, kuma yaci zaɓe, zai yaƙi ƴan ta’adda dukkanin iyawar sa.
Yace “Matsala guda da Gwamanatin PDP (a Ƙarƙashina idan aka zaɓe Ni) zata magance, shine Matsalar Tsaro a Ƙasar, inba haka ba, to babu hanyar da Tattalin Arziki zai bunƙasa.
“Idan ƴan bindiga suka ji Suna na zasu ruga, sabudda zan yaƙe su sosai. Zan zama Mai Kula da Tsaro a Ƙasa.
“Zan riƙa bada umarni akan ayyuka, a tsaro, a Noma, da Tattalin Arziki tare da Sojoji. Zan riƙa bada umarni a kowane ɓangare na rayuwa. Domin ina da ƙwarewar da zan magance matsalolin Najeriya.”