Hukumar tace fina-finai da bidiyo ta ƙasa, NFVCB, ta ce hukumar ta karɓa tare da tace fina-finai 541 da masana’antar fina-finan Nijeriya ta Nollywood ta shirya a farkon kwata ta shekarar 2022.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Adedayo Thomas, Babban Daraktan NFVCB ya fitar a yau Juma’a a Abuja.
Ya ce Sashen Tace Fina-Finai da Tantance wa na hukumar ne su ka fitar da wannan ƙididdiga a cikin rahoton ta na kwata ta farko na shekarar bana.
Thomas ya ce rahoton ya dauki dukkan fina-finan da aka mika wa hukumar daga sassan kasar.
Ya ce za a gabatar da rahoton ga hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa don tattara abubuwan da aka samar na cikin gida, GDP, na kashi na farko na GDP, Q1, 2022.
M Thomas ya ƙara da cewa rahoton kwata na farko ya nuna cewa an samu ƙaruwar fina-finan da aka yi daga 382 a kwata ra karshe na shekarar 2021 zuwa 541, wanda ke nuna ƙaruwar kashi 42 cikin ɗari.
“Mun yi farin ciki da cewa masana’antar ta fara wannan shekara a bisa kyakykyawan tsari kamar yadda aka nuna a cikin karuwar adadin fina-finan da hukumar ta samu don tantancewa da amincewa a cikin kwata na farko.
“Ko shakka babu masana’antarmu ta fim ita ce babbar hanyar da za ta taimaka wa tattalin arzikin kasa, kasancewar fina-finan da ake shiryawa na nuni da irin ayyukan yi kai tsaye da kuma kai tsaye da sashen ke samarwa,”