A Bisa Adalci Shiyyar Daura Ya Kamata A Ba Kujerar Gwamnan Katsina A 2023 – Inji Dangiwa

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dan takarar gwamnan jahar katsina karkashin tutar jam’iyyar APC Arc, Ahmad Musa Dangiwa ya ziyarci Ofishing jam’iyyar domin gabatar da kanshi ga shugabannin jam’iyyar da kuma neman goyon bayansu dangane da yunkurinshi na son zama gwamnan jahar ta Katsina.

Arc, Dangiwa wanda ya kasance tsohon shugaban babban bankin bada lamunin gidaje na Najeriya, tun da farko dai ya fara bayaninsa da bada tarinhin shi da na aikace-aikacen da ya yi da na siyasarsa da kuma yadda ya rike matsayin da shugaba Buhari ya ba shi ba shugabn babban banki bada lamunin.

Ya kuma ce ya zo ne domin ya sanar da su da kuma neman goyon bayansu.

Dangiwa ya kuma ja hankalin shugaban nin jam’iyyar ta APC da su ji tsoron Allah su zabar ma mutane shugaba na gari mai tausayi.

Hakazalika a cikin jawabin na sa ya bayyana cewa a adalci a kujerar gwamnan jahar shiyyar Katsina da Funtua sun yi mulki wannan karon kamata ya yi a ba wani ya zama gwamna daga yankin Daura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram