Duk Wanda Ya San Ni Ya San Ba Ni Da Tarihin Raina Mutane – Sani Danlami

Tsohon Dan majalisar tarayya a katsina ta tsakiya kuma tsohon kwamishinan walwala da jin dadi da wasanni na jahar Katsina, Sani Aliyu Danlami ya ce idan ya sake darewa saman kujerar majalisar tarayya a katsina ta tsakiya zai zama dan majalisar da za a dade ba a samu kamar sa ba a tarihi.

Sani Danlami ya bayyana haka ne a yayin wata fira da manema labarai kamar yadda popular News Hausa ta ruwaito.

Tsohon kwamishinan ya fadi wasu abubuwa goma da ya lissafo zai sanya a gaba idan ya samu kujerar.

Abubuwa goman kamar yadda popular News Hausa din ta zayyano, sun hada da kula da mutanen da suka jajirce don ganin ya kima da mutunta jam’iyyarsa ta APC da kasancewa sahun gaba don magance bukatar mutanen da ya ke wakilta da tsayawa don jin koken al’umma da kula da matasa da jajircewa wajen sauke nauyin jama’ar da ya ke wakilta.

Abu na gaba da ya ce shi ne zai kokari ya ga ya zama Dan majalisar da ba a taba irinsa ba wajen tafiyar da al’amurran jama’a da kuma fitar da jama’ar da ya ke wakilta kunya wajen mikewa ya yi magana.

Danlami ya kuma ci gaba da cewa zai yi huddar siyasar sa cikin tsari da bin doka sai uwa uba tawakkali ga Allah game da takarar ta shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram