An Yi Garkuwa Da Fulani 10 Da Shanu 300 A Anambra.

Wasu Yan bindiga a jahar Anambra sun yi garkuwa da wasu fulani mambobin kungiyar Makiyaya ta Najeriya (MACBAN) guda 10 tare da sace shanu 300.

BBC ta ruwaito, an kai ma Fulanin harin ne cikin dare a yayin da su ke bacci a Obene cikin ƙaramar hukumar Ogbaru a jahar ta Anambra, kamar yadda shugaban Miyetti Allah shiyar kudu maso gabashin Najeriya, Alhaji Gidado Siddiki ya shaida wa jaridar The Nation.

Hakazalika an ce Ƴan bindigar sun kai su 40 ɗauke da manyan makamai inda suk buƙaci a biya su miliyan hudu a matsayin kuɗin fansa da kuma bindiga daga iyalan wadanda aka kama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram