Ana Zaton Bom Ya Tashi A Cikin Daren Nan A Gidan Giya A Jahar Yobe

Wani abin fashewa da ake kyautata zaton bom ne ya fashe a wani gidan giya a karamar hukumar Gashuwa ta jahar yobe a cikin daren nan.

Abin fashewar dai ya hallaka mutum daya tare da jikkata mutane 7

Majiyar Jakdiya ta hanyar Muhammad Bashir Mato, ta nakalto cewa wasu mutane daga garin sun tabbatar da bom ne ya tashi yayin da tuni shugaban karamar hukumar ya kafa kwamiti don binciken lamarin tare da bada umurnin rufe duk wani gidan giya da ke cikin garin Gashuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram