Idan Malam Mannir Yakubu Ya Ga Dama Sai Ya Shiga Masallaci Ya Ci Gaba Da Wa’azi

An kwatanta cancantar mataimakin gwamnan jahar Katsina Mannir Yakubu da mutumin da ya fi kowa cancanta da a bashi jagorancin jahar Katsina a matsayin gwamna.

Wannan na fitowa ne a yayin wani taro da yan jarida da kwamintin wayar da kan jama’a akan takarar mataimakin gwamnan ya yi a ranar Assabar din nan a karkashin jagorancin shugaban kwamitin, Ibrahim Tukur Jikamshi.

Ibrahim Jikamshi ya ce Mannir ya kubu mutum ne na gartacce kuma gogaggen dan siyasa ne da ya yi don ci gaban al’umma.

Hakazalika Jikamshi ya ce yana da ilimi na addini da na boko ya kuma ce shi mataimakin gwamna dambu ne mai hawa biyu wato ga boko ga addini ya kara da cewa ko yanzu malam Mannir Yakubu ya ga dama sai ya shiga masallaci a kafa ma shi lasifika ya ci gaba da wa’azi.

Bayan fadin abubuwan cancanta na mataimakin gwamnan sai kuma ak bayyana da aniyarsa ta zuwa ofishin jam’iyyar APCn jahar domin gabatar da kanshi ga shugabannin jam’iyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram