Rayuka 8 Sun Salwanta, 43 Sun Jikkata A Haɗarin Mota A Madina

Mutane 8 ne su ka rasu, yayin da wasu 43 su ka jikkata a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a birnin Madina a jiya Juma’a.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Red Crescent, reshen Al-Madinah Al-Munawwarah, Ahmed Al-Zahrani ya ce sun samu sanarwar haɗarin da karfe 06:14 na safiyar Juma’a, inda ya bayyana cewa wata motar bas ta kife kan titin babbar hanyar kilomita ta140.

“Nan da nan, a ka kai sabbin motocinmu na agaji masu suna RTA zuwa motar da ta samu haɗarin (Twaiq), kuma tawagar farko ta isa tun ƙarfe 06:24 na safe.”

Tawagar motocin daukar marasa lafiya 20 daga yankunan biyu, da tawaga 6 daga yankin Makkah Al-Mukarramah, tare da wasu tawagogi 26, da tawagogin harkokin lafiya 6 karkashin jagorancin kwamandan filin, da daraktan kula da lafiya, da mai taimaka wa al’amuran gaggawa da masu biyo baya. -har zuwa darektan umarni da sarrafawa ne su ka yi aikin agaji a yayin haɗarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram