Ta’aziyya: Alaafin Ya Tabbatar Da Cigaba A Matsayin Sa Na Uba Ga UNIMAID

Shugaban Jami’ar Maiduguri Farfesa Aliyu Shugaba ya bayyana mutuwar uban Jami’ar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III a matsayin rashi mai zafi.

Shugaba ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi.

Yace marigayi Adeyemi ya nuna irin ƙudirin shi ne cigaban ilmi a Najeriya dama Jami’ar a lokacin da ya kasance Uba ga Jami’ar.

Shugaban Jami’ar yace marigayi Alaafin za’a cigaba da tuna shi akan kyakkyawan Shugabancin sa, da Shawarwari irin na Uban Ƙasa, goyon baya, da fahimta gami da cigaban Jami’ar.

“A yayinda Jami’ar ke kuka na rasuwar sa, a madadin Shuwagabancin ta da Ma’aikata, da Ɗalibai, muna miƙa ta’aziyyar mu ga Shugaban Ƙasa Muhammadu, Gwamnatin Jahar Oyo, da iyalan sa dama Masarautar baki ɗaya.

“Muna addu’a ga Allah daya jiƙansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram