Zaɓar Mu Da Dattawan Arewa Suka Yi A Matsayin Ƴan Takarar Maslaha Na PDP yin Allah Ne – Gwamnan Bala

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya suffanta zaɓar shi da tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki a matsayin ƴan takarar shugaban ƙasa na maslaha a jam’iyar PDP da ga Arewacin Nijeriya a matsayin wani aiki ne na Ubangiji.

NAN ya tawaito cewa a ranar Juma’a ne dai Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi, ta zaɓi Mohammed da Saraki a matsayin ƴan takarar shugaban ƙasa na maslaha da ga yankin Arewa gabanin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da PDP ɗin za ta yi.

Ƙungiyar ta ce ta yi zaɓen ne bisa amfani da wasu ƙa’idoji wajen Tantance ƴan takara huɗu da su ka gabata da kan su da ga Arewa.

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, wanda ɗaya ne da ga cikin ƴan takarar, ya ƙi amince wa da zaɓar Mohammed da Saraki da ƙungiyar ta yi.

Sai dai kuma da yake jawabi ga manema labarai a jiya Asabar a Bauchi, gwamna Mohammed ya ce bai san yadda a ka yi ƙungiyar ta ɗauki matakin zaɓar shi da Saraki ba.

Ya kuma yaba wa ƙungiyar bisa binciken ƙwaƙwaf da kuma yin abinda ya dace.

“Mutane za su zaci cewa ko kun shiga mun fita ne ko mun nema a zaɓe mu. To kwata-kwata ba haka bane. Kawai dai an ga cancantar mu ne kuma ma dai yin Allah ne kawai,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram