Wata mata ‘yar kasar Japan da aka tabbatar a matsayin wacce ta fi kowa tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 119, kamar yadda jami’an yankin suka fada a ranar Litinin.
An haifi Kane Tanaka a ranar 2 ga watan Janairun shekarar 1903, a yankin kudu maso yammacin Fukuoka na kasar Japan, a wannan shekarar ne ‘yan’uwan Wright suka tashi a karon farko kuma Marie Curie ta zama mace ta farko da ta lashe kyautar Nobel.
Tanaka tana cikin koshin lafiya har zuwa kwanan nan kuma ta zauna a gidan jinya, inda take jin daɗin wasannin allo, magance matsalolin lissafi, soda da kuma cakuleti.
A cikin shekarunta, Tanaka ta gudanar da harkokin kasuwanci daban-daban da suka hada da kantin sayar da noodle da kantin sayar da wainar shinkafa. Ta auri mijinta mai suna Hideo Tanaka karni a shekarar 1922 da suka gabata, inda ta haifi ‘ya’ya hudu kuma ta dauki na biyar.
Tsohuwar dai ta yi niyyar yin amfani da keken guragu don shiga cikin wasan ba da wutar lantarki a gasar Olympics ta Tokyo a shekarar 2021, amma cutar da take fama da ita ta hana ta yin hakan.
Lokacin da kundin tarihin duniya na Guinness ya gane ta a matsayin mace mafi tsufa a shekarar 2019, an tambaye ta a wane lokaci ne ta fi farin ciki a rayuwarta. Amsar ta data bayar itace: “Yanzu.”
An bayyana ayyukanta na yau da kullum a lokacin da ya hada da tashin karfe 6:00 na safe, da kuma la’asar inda take karantar darasin lissafin da kuma koyon aikin kiraigraphy.
“Daya daga cikin abubuwan da Kane ta fi so shine wasan Othello kuma ta zama ƙwararriya a wasan allo na gargajiya, sau da yawa tana bugun ma’aikatan gida,” in ji Guinness.
Gwamnan karamar hukumar Seitaro Hattori ya yaba da rayuwar Tanaka bayan ta rasu a ranar 19 ga watan Afrilun 2022.
“Ina fatan ganin Kane-san a kan Girmama Ranar Tsofaffi na wannan shekara (biki na kasa a watan Satumba) da kuma bikin tare da soda da cakulan da ta fi so,” in ji shi a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Ya kara da cewa, “Na yi matukar bakin ciki da samun labarin rasuwar ta.”
Japan tana da yawan tsofaffi a duniya, a cewar bayanan Bankin Duniya, tare da kusan kashi 28 cikin ɗari masu shekaru 65 ko sama da haka.
Matar da ta fi kowa tsufa da kundin littafin Guinness ya tabbatar ita ce ‘yar Faransa Jeanne Louise Calment, wacce ta mutu tana da shekara 122 da kwanaki 164 a shekara 1997.