Farashin Tikitin Jiragen Sama Yayi Tashin Gwauron Zabi, A Dalilin Bikin Sallah

Yayin da ake shirin gudanar da bukukuwan sallah karama a farkon mako mai zuwa, yawancin kamfanonin sufurin jirgin sama sun kara farashin tikitin jirgin sama na cikin-gida.

Sai dai ba dukkan wurare ne wannan karin ya shafa ba.

Matafiya tsakanin biranen Legas zuwa Abuja da Legas zuwa Port Harcourt da kuma Legas zuwa Uyo za su ci gaba da sayen tikitin a farashin da ka iya kai Naira 50,000 da ake biya a baya-bayan nan.

Karin ya fi kamari ne idan matafiyi ya nufi biranen da ke arewacin kasar nan, daga kudanci, inda farashin tikitin ya tashi zuwa Naira dubu Dari da ashirin da biyu, (122,000.00) na zuwa kawai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan mataki zai tilastawa wasu mutane sauya shirin da suka yi na tafiya garuruwansu domin bukukuwan sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram