Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa a ranar Litinin ta tantance barnar da aka yi a wurin da bam din da ya tashi a garin Iware na karamar hukumar Ardo Kola a jihar Taraba.
Fashewar da ta tashi a babbar kasuwar shanu ta kashe akalla mutane shida, a cewar majiyoyin ‘yan sanda, sai dai mazauna yankin sun ce mutane 16 ne suka mutu yayin da 19 suka jikkata.
Shugaban Hukumar NEMA dake kula da Taraba/Adamawa, Mista Ayuba Ladan, wanda ya jagoranci tawagar wajen tantancewar, ya ce tawagar ta je wurin ne domin sanin irin barnar da aka yi da kuma yadda za su shiga tsakani.
Da yake jajantawa gwamnatin jihar Taraba da mutanen da fashewar ta rutsa da su, hukumar ta ce gidaje 121 ne fashewar ta shafa.
Ladan ya ce, “A kididdigar da muka yi, mutane tara ne suka mutu, 28 sun jikkata, wasu da dama kuma sun rasa muhallansu.
“Za mu mika rahoton zuwa hedkwatar domin mayar da martani cikin gaggawa da kuma shiga tsakani ga wadanda harin bam din ya rutsa da su.”