Gwamna Okowa Yace Allah Kaɗai Ne Zai Zaɓi Wanda Zai Gaje Shi

Gwamnan Jahar Delta Ifeanyi Okowa yace a shirye yake ya baiwa Allah zaɓi ya nuna wanda zai gaje shi a shekarar 2023.

Okowa ya bayyana haka a taron Murnar zagayowar ranar haihuwa da Bada kyaututtuka na Chief Oritsetimeyin Adams a Cocin Cathedral Dake Sapele a Ƙaramar Hukumar Sapele.

Gwamnan yace baya da sha’awar ya baiwa mutane suyi zaɓi, amma ya barwa Allah ya zaɓarwa Jahar Gwamnan daya fishi wanda zai gaje shi.

Ya yabawa Cocin da Sauran Shuwagabannin ta da addu’o’i da goyon baya, sai yayi addu’a ga Allah daya zaɓarwa Jahar Gwamnan daya fi cancanta wanda zai gaje shi.

“Zaɓar wanda zai gaje Ni bawai zaɓi na bane ba, amma zaɓin Allah ne.

“Ina addu’a duk wanda Allah yake so ya zama Gwamna, Allah yasa ya zamo ya fini.

Gwamnan ya taya wanda aka shirya wa bikin ranar zagayowar haihuwar daya cimma Shekarun, sai ya buƙace shi daya maida hankali wajen yiwa Allah bauta da Al’umma baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram