Hukumar Kashe Gobara A Kano Ta Samu Nasarar Ceto Ran Bujimun Zakaran Da Ya Faɗa Rijiya

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto rayuwar wani Dattijon zakara dan shekara 1, bayan da ya fada rijiya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ya aikowa da jaridar Dimokuradiyya ya ce sun Sami nasarar ki tar da zakaran ne bayan sun Sami Kiran gaggawa.

Zakaran da hukumar tasu ta ceto dai ya fada rijiya ne a unguwar Kwalli dake karamar hukumar birnin Kano.

Saminu Ya ce jami’ansu sun ceto zakaran kuma tuni suka mika shi ga wanda yake kula dashi.

A karshe hukumar kashe gobarar ta ja hankalin alumma da su dinga rufe rijiya gudun abinda kaje yazo.

 

Wanna kokari dai tuni ya fara samun yabo daga alummar jihar, duba da yawancin Hakan wato dai ceton ran Dabba aka fiya samun labarin kasashen ketare

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram