Masarautar Kano Ta Bukaci Hakimanta su Shiga Kwaryar Birni Don Bukukuwan Sallah

Masarautar Jihar Kano ta bayar da umarni ga daukacin hakiman Masarautar da su kasance a cikin kwaryar birnin Kano domin gudanar da bikin hawa sallah Ƙarama na bana.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Alhaji Awaisu Abbas Sanusi a madadin sakataren Masarautar. Wadda kuma aka raba ta ga manema labarai a yau Talata.

Sanarwar ta kuma bukaci daukacin Hakiman da su taho cikin birni tare da Dagatan su, da kuma Dawakansu, da sauran mahayansu, a ranar Juma’a wato 28 ga Ramadan, dai dai da 29 ga watan Afrilu, 2022.

Kazalika sanarwar ta kuma umarci hakiman da su da suje Fadar Sarkin Kano a ranar Asabar 29 ga watan Ramadan, da karfe 11 na safe, domin karbar Umarni daga mai martaba.

Bayan wannan taro Hakiman za kuma su kara haduwa domin wani taro na musamman a dakin taro na musamman na Masarautar Kano, dake kofar Kudu domin yi musu bayani kan yadda Hawan zai kasance.

Tuni dai Masarautar Kano ta sanar da shugabannin ƙananan hukumomin Hakiman domin samun sauƙin gudanar da al’amuran da suka sanya gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram