Masari Ya Naɗa Muntari Lawal Sakataren Gwamnatin Katsina

Gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari ya bai wa Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jahar Katsina, Muntari Lawal riƙon Ofishin sakataren gwamnatin jahar.

Wannan na cikin wata sanarwa da babban Daraktan kafafen zamani na gwamnan, Al’amin Isa ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta kuma ce Muntari Lawal zai fara aiki a matsayin muƴaddashin sakataren gwamnatin nan take.

A satin da ya gabata ne dai tsohon tsohon sakataren gwamnatin Mustapha Inuwa ya sanar da aje muƙamin domin samun damar yin takarar gwamnan Katsina da ya ke da gurin yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram