Naci Amanar Ƴan Ƙasata Najeriya Idan Ban Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa Ba – Osinbajo

Mataimakin shugaban Muhammadu Buhari na Najeriya Yemi Osinbajo ya ce ya ci amanar kasar idan bai tsaya takarar mukamin shugaba kasa ba a 2023.

Farfesa Osinbajo ya yi wanan kalami ne a yayin wata ziyara da ya kai jihar Ondo, inda ya gana da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.

Ya na mai cewa rike mukamin mukaddashin shugaban kasa da ya ke yi a wasu lokuta ya ba shi kwarewar da yake bukata domin ya jagoranci Najeriya.

A labarin BBC Hausa, ta ruwaito cewa Osinbajo ya ci gaba da cewa, “Mutane na mutuwa a kowace rana, saboda haka zai kasance cin amanar kasa idan na yi ritaya kuma na koma Legas ko Ikenne bayan wa’adin mulkinmu. Ban yi wa kasar nan adalci ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram