Tsohon Shugaban Jam’iyyar APGA Victor Umeh ya jaddada cewa babu adalci idan yankin Kudu Maso Gabas Bai samar da Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023.
Umeh ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Gidan Talabijin na Channels a Shirin Siyasar mu a Yau a ranar Litinin.
A yayinda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda ɗan Asalin Jahar Katsina zai kammala wa’adin mulkin sa na biyu a Shekarar 2023, akwai kiraye-kiraye daga Gwamnonin Yankin Kudu nason a fito da Shugaban Ƙasa a yankin.
Majiyar Jaridar Jakadiya ta gano cewa, tuni Gwamnonin Kudu suka haɗa kai inda suka ce dole a fito da Shugaban Ƙasa daga yankin su.
“Yankin Kudu maso Gabas Bai taɓa fito da Shugaban Ƙasar Najeriya ba.
“Babu wani daga yankin Kudu maso Gabas daya taɓa zama Shugaban Ƙasa, yanzu juyowar yankin ne na samar da Shugaban Ƙasa.
“Ta hanyar da muka miƙa mulki na tsawon shekaru, zaka ga cewa yankin Kudu maso Yamma ya taɓa samar da Shugaba Obasanjo na tsawon shekaru 8, yanzu suna da Mataimakin Shugaban Ƙasa maici na tsawon shekaru 8 da Buhari, yankin Kudu maso Kudu ya samar da Shugaban Ƙasa wato Jonathan wanda ya kusa Shekaru 6,” Inji shi.