2023: Bazan Taɓa Ajiye Ƙudirin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa Ba, Nafi Kowa Dacewa — Kalu

Shugaban Masu Horaswa na Majalissar Dattijai ta Najeriya Orji Uzor-Kalu yace bai ajiye aniyar sa ta tsayawa takarar Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023, kamar yadda wasu Kafafen Yaɗa Labaru suka ruwaito.

Yace zai yi Takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC idan har Jam’iyyar ta bada tikitin ta ga Yankin Kudu maso Gabas.

Kalu, wanda yayi bayani akan Jawabin da aka fitar a ranar Talata, ya bayyana cewar adalci ya buƙaci Yankin Kudu maso Gabas ya samu Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC.

Yace ” Abunda nake tsaye dashi ba ɓoyayye bane Ban ajiye ƙudirina na Tsayawa Takara ba, kuma bazan taɓa ajiye wa ba.

“Ina kira ga ƴan uwana daga Yankin Kudu Maso Kudu da yankin Kudu Maso Yamma su fito ƙwansu da kwarkwata su nemi Kujerar Shugaban Ƙasa amma su ajiye, su goyi bayan mu domin Adalci.

Kalu yayi kira ga Ƴan Siyasa da suke neman Kujerun Siyasa a Ƙasa dasu sanya Zaman Lafiya da haɗin kai fiye da ƙudirin su na tsayawa takara.

Ya jaddada cewa baza’a taɓa cimma wani cigaba ba, ba tare da zaman lafiya ba a tsakanin ƴan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram