2023: Tinubu Ya Buƙaci Masoyan sa Dasu Yiwa Buhari Addu’a ya magance matsalolin Najeriya

Jigon Jam’iyyar APC na Ƙasa Bola Tinubu yayi kira ga Magoya bayan shi dasu amfani da wannan wata na Ramadan domin yin Addu’a ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya samu nasarar magance matsalolin tsaro dake fuskantar Ƙasar.

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasar yayi wannan kiran a cikin wata sanarwa daya fitar daga mai Taimakawa Tinubu akan yaɗa labaru.

A lokacin da yake yabawa Majalisar Dokokin Jahar Lagos da sauran magoya bayan shi akan ƙudirin su da suka yi na shirya wata addu’a a gare shi, Tinubu yayi kira a garesu dasu riƙa addu’ar ga Najeriya da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Sanarwar tace ” a matsayin ku na Musulmi Ku cigaba da Azumin ku da Addu’o’i ga Allah a wannan wata mai Albarka, ina godiya ga Majalisar Dokokin Jahar Lagos da suka shirya Ɗawafi da addu’a a gareni a yau (Alhamis) a Makka.

“Ina jindaɗi ga wannan karamcin ga addu’a ga Allah daya Albarkaci Takara ta domin jan ragamar Ƙasar daga Shekarar 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram