Akalla shanu 113 ne aka sace tare da jikkata wasu makiyaya biyu a wani sabon hari da aka kai a kusa da kauyen Kpara da ke unguwar Tahu a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Shugaban kungiyar GAFDAN a karamar hukumar Bassa, Abubakar Abdullahi Buba, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce barayin sun kuma harbe shanu shida har lahira.
Ya ce an kai harin ne da misalin karfe 3 na rana a lokacin da makiyayan ke gudanar da kiwo kamar yadda suka saba.
Ya bayyana sunayen wadanda abin ya shafa da Abubakar Musa da Inusa Musa.
Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ (OPSH) da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, “Eh, sashen na 3 na Operation Safe Haven ya tuntubi kungiyoyin biyu yayin da aka kwato wasu shanu.
Sannan yace ana ci gaba da sasantawa cikin aminci dan shiga tsakani.
“An yi kira ga kungiyoyi daban-daban da kada su dauki doka a hannunsu saboda ana kokarin kama wadanda suka aikata laifin.”