Yanzu Haka Akwai Kuri’u Miliyan 11 Da Ke Jira Na A Zaɓen 2023 – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya buƙaci jam’iyyar PDP ta sake bashi dama a zaben fitar da gwani na shugaban ƙasa da za a gudanar.

Alfijir Radio ta ruwaito cewa Atiku yana wannan jawabi ne a gaban shugabannin gudanarwar jam’iyyar a ranar Alhamis, inda ya ce ya kamata jam’iyyar ta yi la’akari da cewa, yanzu haka yana da kuri’u miliyan 11 da ke jiransa.

Ya ƙara da cewa ‘yan Nijeriya su saka ransu a inuwa domin za su samu kyakkyawan jagoranci daga PDP duba ga yadda kwamitin gudanarwar ke tafiyar da harkokin jam’iyyar lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram